Posts

FITOWA TA 1. *Daga Littafin:AUREN MUTU'A A WAJEN YAN SHI'A. *JERIN LITTAFAN SHI'A 4. *WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah). *YÃDÃWA:- www.jibwisbirnin-magaji.blogspot.com  بسم الله الرحمن الرحيم MA'ANAR MUTU'A:AUREN WUCIN GÃDI               Mutu'a,ko kuma auren wucin gãdi,watau auren da ba na dun-dun-dun ba,ma'anarsa shi ne namiji ya kulla jinga da mace cewa zai sãdu da ita sau daya ko sau biyu,ko kuma na tsawon awa daya,ko kwana kaza,ko wata kaza,akan kudi kaza ko lãdan abu kaza.               Auren Mutu'a yana cikin aurace-auracen Jahiliyya kuma anyi aiki dashi a farkon Musulunci kãna daga bisãni aka haramta shi.An karbo ruwãya daga Ali binu Abi Dalib(R.A),cewa "Manzon Allah(S.A.W) ya hana auren Mutu'a da cin naman jakin gida a lokacin (yakin)khaibar.''(Bukhari da Muslim).               Amma yan Shi'a sun ci gaba da halasta Mutu'a kuma sun kãgo ruwayoyin karya ...